Idan Har Ka Kubutar Da Wanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Jirgin Kasa Zan Zabe Ka Da Jinin Jikina, Cewar Mansurah Isah Ga Tinubu


Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Mansurah Isah cikin kakkausar sanarwa ta yi kira ga 'yan takara musamman masu son shiga gwamnati da su yi gaggawar fitar da mutanen da aka yi garkuwa da su idar har suna son a Zabe su. 


A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafin ta na Instagram jarumar ta yi kalamai Kamar haka, 


"Zuwa ga mai girma Ahmad Bola Tinubu, wallahi-wallahi idan har ka taimake mu ka kubutar da matafiyan da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja to ni Mansurah Isa zan zabe ka. Dangina da iyalaina duka za su zabe ka mutanen unguwar mu za su zabe ka wanda suke a cikin kungiyar mu da kuma wanda kungiyar ta taimakawa duk za mu zabe ka."


Ni zan zabe ka da jinin jikina. Domin zaka iya yi zaka iya basu kudaden da suka nema. Kayi amfani da kudin da za ka yi kamfen ka kubutar da su, mu kuma za mu tallata takarar ka kyauta. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post