Yanzu-yanzu: Sarkin Daura mai shekaru 91 ya kara yin wuff da budurwa 'yar shekaru 22


Labari mai zafi da ke zuwan mana yanzu shi ne na yadda Sarkin Daura, Alhaji Dr. Umar Faruk ya sake yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22 a duniya.


Kamar yadda @fashionseriesng suka bayyana, an yi bikin ne ba tare da wata hayaniya ba a makon da ya gabata.


A wani labari na daban, Daily Nigerian ta ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.


An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano. Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.


Idan ba ku manta ba shekarar da ta wuce lokacin sarkin yana da shekaru 90 a duniya ya ya auri wata budurwar mai shekaru 20 inda yanzu ya kara da wata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post