Mahara Sun Sace Matar Ma’aikacin Poly Da ’Ya’yanta 3 A Kaduna


Wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace matar wani ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna.


Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan sun sace matar ce, Fatima Isah tare da ’ya’yanta uku – Juwairiyya, Safiyya da Fatima yayin harin da suka kai garin Shika na Karamar Hukumar Giwa ta jiha.


AMINIYA ta ruwaito cewa, wani jami’in kungiyar ’yan sintiri da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun afka garin ne da misalin karfe 11 na dare inda suka zarce gidan wadanda lamarin ya shafa salin alin.


Ya ce yayin aukuwar harin ne suka sanar da jami’insu kuma aka yi wa maharan tara-tara inda aka toshe dukkan hanyoyin shiga da fita na kauyen.


“Mun sanya mutanenmu a hanyar shiga kauyukan Karau-karau da Sako don hana maharan tserewa.


“Ganin haka ya sa maharan suka bude wuta inda suka yi ta harbe harbe.


“Sai dai daga bisani bayan mun kusa yin galaba a kansu, sai suka ranta ana kare suka bar yarinya guda daya cikin ’ya’yan matar da suka sace.


Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Alhaji Zubairu Alhassan Zico, ya ce ya samu rahoton kai hari a gidan wani Alhaji Isa Umar, wanda ma’aikaci a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a daren Juma’ar da ta gabata.


Alhaji Zico wanda ya yaba wa kokarin ’yan sintirin, ya jaddada kudurinsa wajen yin duk mai yiwuwa don ganin an ceto wadanda aka sace.


Ya bayyana cewa, yanzu haka jami’an tsaro tuni sun fantsama neman wadanda aka sacen a dazukan da ke yankin.


Duk kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalinge ya ci tura kasancewar bai amsa kiran wayarsa ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post