Masu garkuwa da ni sai da aka basu naira miliyan 100 kafin su sako ni, cewar Hassan Usman


Maharan da suka kai harin ba ‘yan bindiga ne na yau da kullun ba, ‘yan kungiyar ta’adda ne ta Boko Haram.


 “Suna da makamai sosai kuma sun kwace wani yanki mai fadin gaske na dazuzzukan kasar wanda ya kai kusan jihohi uku zuwa hudu tare da ‘yan fashi na yau da kullum wadanda suke dauke da manyan makamai.


 “Masu garkuwa da mu, wadanda daga baya suka koma yi mana bulala a kullum sun Kwara wajen iya duka da kyau. 


“Suna ciyar da mu da naman saniya, har ma sukan ba mu 10,000 kowanne don kula da kanmu. 


"Sun zargi gwamnati da kamawa tare da tsare mambobinsu ba bisa ka'ida ba. Wanda hakan yasa suka ki amincewa su sake mu. 


Iyalina sun biya Naira miliyan 100 domin a sake ni. Cewar Hassan Lawan Usman daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post