Yadda wani mutum ya bankawa gidansa wuta ya kone kurmus a dalilin rikici da matarsa


Wani mutum da har yanzu ba a  bayyana sunan sa ba, kuma mazaunin Lekki Face One, a unguwar Eyenkorin a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya kona gidan sa kurmus.


Mummunan lamarin, a cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hakeem Adekunle, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:28 na safiyar Lahadi.


Ya ce, wani Mista Kola da ke zaune a unguwar, shi ne ya yi gaggawar kiran hukumar kashe gobara, domin sanar da su tashin gobarar.


Jami’an kashe gobara ya kuma ce, sun kashe gobarar a kan lokaci tare da hana ta tashi zuwa wasu gine-gine.


Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa, mutumin ya ce: “Da gangan ya watsa man fetur a dakunan na sa guda uku, sannan ya banka wuta saboda takaicin matarsa.”


Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kara sanya ido a gidajen su ko ofisoshin su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post