Yanzu-Yanzu: Baza Ayi Hawan Sallah A Masarautar Katsina Ba, Cewar Mai martaba


Majalisar masarautar Katsina da Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ke jagoranta ta fitar da sabuwar sanarwar cewa ba za'a yi hawan Babbar Sallah ba na shekarar 2022 ba. 


Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa ta manema labarai dauke da sa hannun Sarkin Tsaftan Katsina, Alhaji Sule Mamman Dee a ranar


Jaridar Katsina Daily Post ta rawaito cewa a cikin sanarwar, masarautar ta ce Mai Martaba Sarki zai je Masallacin idi ne kawai yai sallah amma ba za'a yi bukukunan sallah ba kamar yadda aka saba gabatarwa ba. 


Daga karshe sanarwar ta yi kira ga al'umma da suyi addu'o'i na Musamman a duk inda suke domin neman zaman lafiya a kasarmu jihar katsina da makotan ta da ma Najeriya baki daya. 


Mai karatu dai zai iya tuna cewa a satin da ya gabata, masarautar ta fitar da sanarwa inda ta ce mai martaba sarkin ba za ayi hawan bariki ba kamar yadda aka saba duk shekara amma dai zai yi hawan sallah.


Sanarwar dai ba ta rasa nasaba da matsalolin tsaro da jihar ta dade tana fama dashi wanda har kawo yanzu ba'a iya shawo kan lamarin ba. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post