Bazan Iya Yima Kowa Mataimaki Ba - Kwankwaso


Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce takaddamar wanda zai yarda ya zama Mataimaki ce ta rusa batun kawancensa da dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi.


Kwankwaso ya ce dalilin da ya sa ya ki amincewa ya karbi mukamin mataimaki shi ne muddin ya yi haka, to jam’iyyarsa ta NNPP za ta iya mutuwa.


Tun a kwanakin baya ne dai ake ta raɗe-raɗin cewa akwai yiwar za'a iya hadewa tsakanin sanata Rabi'u Kwankwaso da takwaransa na jam'iyar Labour Party Peter Obi. Sai dai shi Peter yaki amincewa ya zama mataimaki sai dai shi Kwankwaso ya zama mataimakin sa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post