Yadda Aka Cafke Wani Matashi Ɗan Damfara Da Yake Yin Shigar Mata Yana Jan Hankalin Maza


Matashin da aka cafke shi yana kokarin kutsa kai cikin wata Kotu a matsayin shi mace ne, amma masu gadin wajen suka yi kokarin dakatar dashi inji Ojodu, wani mamba na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) dake Lagos.


Bayan tsawon bincike anan suka gano cewa akwai alamar tambaya game da wannan dake nuna shi mace ne, anan masu gadin wajen suka cire kayan jikin sa inda suka gano cewa katon gardi ne da yai shigar mace.


"Ba musan dalilin sa na yin hakan ba, amma dai mun mikashi wajen ƴan sanda domin gudanar da bincike akan sa, cewar Ojodu."


Mun samu wayar hannu guda 3 daga wajen sa da kuma wasu abubuwa da dama. Ya sanar mana da cewa shi dan damfara ne yana da akawun na facebook da yake amfani dashi wajen yaudarar al'umma a matsayin mace.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post