Kotu ce kaɗai za ta rabani da wanda sukai min Kazafin cewa tsananin Rashin lafiya ke damuna


Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye a cikin shirin nan mai dogon zango na Dadin Kowa da Arewa 24 suke haskawa, yana shirin garzayawa Kotu don kai karar wanda ya bayar da labarin cewa ba shi da lafiya.


A bayan nan ne dai wani labari ya bayyana cewa rashin lafiyar ta jawo mawaki Hamisu Breaker ya ba shi miliyan biyar, sannan kuma jarumi Ahmed Lawan ya ba shi Naira dubu dari biyu don ya nemi magani.


A wata hira da akayi da kamaye a jaridar Aminiya, Dan Azumi Baba ya ce zai dauki matakin ne don kotu ta bi masa hakkinsa kan wannan kazafi da ake yadawa a kansa.


Ya ce, Wannan ba shi ne karon farko ba da wannan mai labaran karya ya ce ba ni da lafiya ba, kuma an bani wasu kudade don neman magani.


“A baya, cewa ya yi gwamnatin Jihar Kano ta yi min alkawarin miliyan biyar in nemi magani, sannan kuma ya sa hotona da na gwamnan Kano da kuma na Baba Impossible a bidiyon. Sai kuma yanzu ga wannnan sabon kazafin.”


Tuni Dan Azumi Baba ya aika da wani sako na wannan aniya ta sa ga Kungiyar Dattawan ‘yan fim tare da nemansu da kar su sa baki domin ba zai hakura ba.


A cewarsa, ya aika sakon aniyarsa tasa ce ga Kungiyar Dattawan don ko a nan gaba mai wannan batancin zai nemi da su sa baki ya janye ganin cewa ya dauki mataki na shari’a.


Kamaye ya ce tuni sun gama magana da lauyansa kuma nan ba da dadewa ba za su gurfana a gaban da alkali da mai wannan Kazafi.


Tun a wancen makon ne dai ake ta yada labarin cewa Kamaye yana cikin tsananin rashin lafiya wanda har ta kai ga bai san wanda yake kansa ba, wanda daga bisani ya fito ya karyata hakan inda yace shi yana kasar Niger ma a lokacin ya kai ziyara.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post