Shatu Bawa Matar Da Tayi Fice Wajen Raye-Raye Da Girgiza Mazaunai A TikTok Ta Rasu


Akwai wata Matashiyar bazawara da ta kware sosai a Tiktok tana rawa da girgiza tana juya mazaunanta yadda ta ga dama a TikTok mai suna Shatu Bawa ta rasu. 


An wayi gari bata duniya, Allah Ya karbi rayuwarta, ta mutu ta bar bidiyon rashin albarka da tayi a Tiktok, bidiyon zai tabbata a yanar gizo har a tashi Duniya. 


Wannan yana daga cikin abinda matan Tiktok da sauran masu fitsara a media suka kasa ganewa, duk abinda aka daurashi a yanar gizo ya hau kenan, zai tabbata a Internet har zuriyarku su kare gabaki daya a doron duniya


Kinzo kina rawa kina juya duwawu a Tiktok ba kunya ba tsoron Allah, shin ba kya tunanin 'ya'yanki da jikokin ki zasu zo su gani? ba kya tunanin ko a cikin zuriyarki akwai babban Malami ko wani babban mutum da zai shahara?


Mutuwar wannan 'yar Tiktok wa'azine da ishara, gashi yanzu ba za'a tunata da komai ba sai rawan fitsara, Allah muke roko Ya yafe mata. Allah Ka shiryar da masu fitsara a TikTok ya ganar dasu amin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post