An Yanke wa Wasu Ƴan Luwadi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Jefe Su A Jihar Bauchi


Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan ta same su da laifin yi wa wasu yara luwadi, a Ningi da ke jihar Bauchi.


Duk da dai Lauyoyi sun soki shariar da cewar ba'a baiwa wadanda ake zargin Lauyoyi ba bare har su yi kokarin basu karya ba a karkashin hujjoji.


Kotun ta jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da ya kai sama da shekara 70 da haihuwa, da wannan laifi, wanda suka amsa.


Kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.


Kwamandan Hisbah na karamar hukumar ta Ningi, Adamu Dan Kafi, ya sheda wa BBC cewa, an kama mutanen ne a kauyen Wada a watan Mayu, bayn da suka yaudari yaran da dabino da kuma kwakwa.


Daga Kamal Aliyu Sabongida

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post