Wani Mutum A Zamfara Da Ya Auri Jikarsa Har Sun Yi Yaya 8 Yace Ba Zai Iya Rubuwa Da Ita Ba


Alhaji Musa Tsafe wani magidanci dan jihar Zamfara mai shekaru 47 ya dage akan cewa ba zai saki jikar tasa ba wacce suka yi aure tare har tsawon shekaru 20 tare da haihuwar yaya 8.


Musa wanda dan asalin karamar hukumar Tsafe ne ta jihar Zamfara ya bayyana cewa ba zai iya sakin jikar tasa ba duk kuwa da irin nuna masa haramcin yin hakan a musulunci amma yace sam ba zai sake ta ba. 


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, jikar tasa mai suna Wasila Isah yar garin n Tsafe yar shekaru 35 da haihuwa ta haife masa yara su 8 a tsawon shekaru 20 da suka yi tare a zaman mata da miji. 


Sai dai masana addinin Islama sun sanar da masarautar Tsafe akan lallai a raba wannan auren domin kuwa ya saba da koyarwar addinin musulunci. Hakan ya jefa rudani da sanin me zai je ya dawo ga ma'auratan. 


Malamai masana addini da shugabannin al'umma da suka gayyaci ma'auratan domin yin bincike akan al'amarin sun gano cewa akwai harmaci a wannan auren kuma ya sabawa shari'a. 


Wanda hakan yasa aka baiwa Musa Tsafe umarnin ya saki matarsa domin ba zai yu su ci gaba da zama ba, amma Musa ya bayyana cewa ba zai iya rabu da matar tasa ba. 


Sai dai malaman sun bayyana 'ya'ya 8 da ma'auratan suka haifa a matsayin halattattu, amma sun ce auren ba zai cigaba da tafiya ba tilas a raba shi. Domin aure tsakanin su bai halatta ba. 


Bayan Alhaji Musa ya nuna rashin yarda ga wannan hukuncin da malaman suka yi yasa aka mika shi ga hukumar Hisbah ta karamar hukumar Tsafe, wanda su kuma daga nan suka kai shi kotun musulunci wanda ta saka ranar 21 ga watan Yuli a matsayin ranar da za'a cigaba da Shari'a. 


Hakan ne yasa Alhaji Musa ya garzaya wajen shehin Malami na darikar Tijjaniya, Dahiru Usman Bauchi inda yace anaso ai masa harmaci shi da matarsa. 


Sai dai shi ma Dahiru Bauchi ya tabbatar wa da Alhaji Musa cewa wannan auren nasu haramunne kuma abinda malaman suka fada gaskiya ne babu aure tsakanin su. 


Sai dai shi Alhaji Musa yace shi da matarsa mutu karraba babu wanda zai raba su. Yanzu dai abin jira a gani shine hukuncin da kotu za ta yi akan wannan al'amarin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post