Matar da ke bayar da hayar kayan biki da shagulgula a Kano


Wata matashiya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya da ta bude shagon bayar da hayar kayan biki da mata ke sanyawa a lokutan bukukwansu.


BBC Hausa ta rawaito Habiba Yusha'u wacce akafi sani da Beebas Glam, ta ce ta fara sana'ar ce bayan fahimtar yadda mata ke kashe kudi wajen sayan kayan tufafi yayin bikinsu wanda kuma ba su bukatar shi bayan bikin.


"Idan akayi lakari a kasar Hausa kusan duk bikin da za a yi, za ka ga amarya ta saka tufafi wanda sau daya kawai ake daura shi domin idan ta saka shi bayan biki za'a rika mata kallon mahaukaciya".


Habiba tsohuwar mai sana'ar kwalliya ce amma a yanzu tafi mayar da hankali ne wajen bayar da hayar kayan amare lokacin bikinsu.


Matashiyar ta ce akwai duk irin kayan da amarya ke bukata kuma cikin farashi mai sauki saboda ta fara sana'ar ce domin taimakawa talakawa da marayu tun da ita ma marainiya ce.


Sana'ar bayar da hayar kayan biki Ko suna Ko daurin aure ta zama ruwan dare a birnin Kano, domin yanzu amarya Ko ango suna da damar zuwa shagunan da ake bayar da hayar irin wadannan kayan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post