Wani Mai Halittar Mata Maza Da Ake Tunanin Mace Ne Ya Yiwa Fursunoni 2 Ciki A Cikin Kurkukun MataDemi Minor an dauke shi daga cikin fursuna mata inda aka mayar dashi cikin Kurkukun maza biyo bayan samun sa da aka yi yaiwa wasu fursunoni mata 2 ciki a Kurkukun mata dake New Jersey ta Amurka. 


A rahoton da Daily Nigerian ta wallafa ta rawaito cewa Minor an yanke masa zaman shekaru 30 ne a zaman gidan yari biyo bayan kashe mutumin da ya raine shi a matsayin uba. An dauke ta daga gidan gyaran hali na Edna Mahan zuwa gidan gyaran hali na matasa na jihar a watan Yuni.


Ana tsare da ita a wani waje mafi kazanta a gidan yarin.


Matashiyar mai shekaru 27 da haihuwa, ta koka da yadda masu gadi suka yi mata ba daidai ba da cin zarafi a lokacin canja gidan yarin, har ma an sanya ta a cikin fursunonin da a ke sa musu idanun don kada su kashe kansu bayan ta yi kokarin rataye kanta a lokacin da ake kai ta GSCF.


A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Justice 4 Demi, Minor ta yi ikirarin cewa jami’an gidan yarin na fakon ta, inda daya daga cikinsu ya yi mata ba’a a lokacin da a ka ce a tube mata kaya domin bincikar ta.


A wani rubutu na daban, ta yi zargin cewa an yi mata dukan tsiya a lokacin canja mata gidan yarin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post