Jihar Katsina Ba Za Ta Taba Yafewa Dan Bindiga Ado Aliero Ba, Cewar Gwamna Masari


Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu gwamnatin Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba, dan bindigar da ta ke nema ruwa a jallo duk da nadin sarautar da aka yi masa a Zamfara.


Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ne ya shaida wa gidan jaridar BBC Hausa cewar, sun yi mamakin jin nadin sarautar da aka yi masa, sai dai ya ce ko da a ce Ado Aliero ya daina ayyukan ta'adanci a Zamfara har yanzu a wajen su bai daina ba.


Ya bayyana cewa tun bayan faruwar wannan lamari, ya yi kokarin tuntubar gwamnan Zamfara Bello Matawalle, amma bai same shi ba domin tattauna wannan batu ba.


Gwamna Masari ya ce har yanzu gwamnatin Katsina na kan bakarta ta neman Ado Aliero ruwa a jallo bisa zargin kashe mutanen Kadisau da kashe mutanen Faskari.


A ranar Lahadi ne dai aka yi bikin nadin sarauta ga kasurgumin dan bindiga Ado Aliero a jihar Zamfara wanda ya jawo cece-kuce a kafafen yada labarai. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post