Marayu da yaran talakawa 63 za su yi karatu kyauta a kasar Malaysia


Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dauki nauyin karatun wasu yara marayu da yaran talakawa su 63 karkashin Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, a wata babbar Jami'ar kasa da kasa ta Albukhary da ke kasar Malaysia.

 

A yayin da yake bankwana da wadannan dalibai a fadar gwamnatin da ke Sakkwato, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sakkwato) ya godewa Allah akan wannan nasara da aka samu tare da yin kira gare su da su yi karatu tukuru, domin su kammala cikin nasara, kuma su koma gida su amfani kawunansu da al'ummar jiha baki daya.


Gwamnan wanda ya kara godewa Syed Moukhtar Albukhary wanda shi ne ya assasa makarantar domin 'ya'yan talakawa da marayu su amfana, ya kuma nemi daliban su kasance jakadu nagari masu bin dukkanin ka'idodi da dokar kasar Malaysia.


Shi ma a nasa jawabin, shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) ya bayyana cewa, an zakulo wadannan yara ne daga gundumomi 87 a kananan Hukumomin jihar 23. 


Shugaban ya ce, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta biyawa kowanne yaro Naira Miliyan 2 da dubu 387, tare da basu sabuwar kwamfiyuta da jakunkunan sa tufafi, domin samun saukin karatu.


Shugaban Jami'ar Albukhary Farfesa Dato Abdul'Aziz Tajuddin ta manhajar Zoom, ya godewa Gwamnatin Jihar Sakkwato a kan taimakon marayu da 'ya'yan talakawa da take yi, sannan kuma ya jinjina wa Hukumar Zakka da Wakafi a kan horar da yaran saboda yadda ake fuskantar kalubalen karatu a kasashen waje. 


Kafin su tashi zuwa Babban Birnin Tarayya don cillawa zuwa kasar Malaysia, sai da daliban suka ziyarci Mai Alfarma Sarkin Musulmi a fadarsa inda ya yi musu addu'a da fatan alheri, sannan ya bai wa kowanensu kyautar kudi ta musamman dan karawa a kan guzurinsu. 


Daliban da suka shafe watannin ana horar  da su a fannoni daban daban don fafatawa ta sauran daliban da za su hadu da su a kasashe daban daban na duniya.


Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sakkwato

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post