Gwamnatin Najeriya Ta Kara Farashin Kudin Man Fetur Daga N165 Zuwa 179 A Lita Daya


Har zuwa wannan lokacin hukumar dake kula da Albarkatun Mai na Ruwa da kan Tudu ta kasar da ake kira NMDPRA ba ta ce komai ba biyo bayan matakin da da gwamnati ta dauka na karin farashin kudin man fetur. 


Wasu rahotanni dake yawo na nuna cewa sabon farashin man ya fara aiki ne tun a ranar Talata inda gidajen mai na yankunan kudancin kasar tuni suka fara sayarwa akan sabon farashin N179 daga N165. 


A wasu yankunan ma rahotanni sun nuna cewa ana sayar da man akan N184 wasu kuwa har akan N189 wanda hakan ke nuna an samu karin kusan N24 akan Lita 1.


Za a ci gaba da sayar da man fetur din akan Naira 179 a yankin tsakiyar arewacin kasar, yayin da a birnin Lagos za a ci gaba da sayar da farashin akan Naira 169, sannan kuma a Abuja farashin zai kasance akan Naira 174.


Dama dai tun a shekarar da ta gabata ne dai mahukunta a kasar ke bayyana cewa Za'a yi karin kudin mai wanda hakan yasa aka dinga wahalar man fetur din  fadin kasar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post