'Yan Bindiga Sun Fasa Gidaje Sun Kwashe Matan Aure 4 A Katsina


'Yan bindiga sun fasa gidaje sun kwashe matan aure 4, tare da yara 5 a garin Dutsin-ma na jihar Katsina a cikin dare.


Wasu 'yan bindiga masu yawan gaske dauke da muggan makamai sun kai hari cikin daren ranar Lahadi ana maka ruwa a Unguwar rukunin gidajen Shema da ke cikin garin Dutsin-ma.


Majiyar Katsina Post ta tabbatar mana da cewa a harin da suka kai sun fasa gidaje 3 a unguwar, kuma sun kwashe matan aure hudu ciki hadda mai ciki da ake sa ran za ta haihu yau ko gobe da wasu mutane biyar suka tafi da su daji.


Gidajen da 'yan bindigar suka shiga sun hada da na wani Malam Abubakar Lawal inda suka tafiyar da matan sa biyu da ya'ya biyu sai gidan wani jami'in kwastam, Usman Abdulaziz, wanda aka fi sani da Shagari inda suka tafi da matansa biyu da wasu mutane uku.


Majiyar mu ta cigaba da cewa gida na uku da 'yan bindigar suka shiga basu iske kowa ba, domin mai gidan da matar su duk sun gudu da suka ji zuwan tsagerun.


Rundunar yan sandan Najeriya dake Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin mai magana da yawun ta SP Gambo Isah amma ya ce kawo yanzu ba su da cikakken bayani kan lamarin suna jiran bayanan daga baturen yan sandan karamar hukumar.


Garin na Dutsin-ma dai na fuskantar karuwar hare-haren yan bindiga tun bayan rasuwar Kwamandan yan sandan shiyyar, ACP Aminu Umar a kimanin sati biyu da suka gabata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post