Wani maniyyaci da bai samu shiga rukunin ƙarshe da jirgi ya ɗiba zuwa ƙasa mai tsarki ba, ya ayyana cewa zai gudanar da aikin Hajjinsa cikakke a sansanin Alhazai da ke jihar Kano.
Malam Jibrin Abdu daga garin Gezawa ya zama abun kallo bayan an gan shi cikin shigar farin Harami kuma ya bayyana cewa tuni ya fara aikin Hajjinsa a sansanin.
Ya ce ya siyar da Gonarsa domin ya samu damar zuwa sauke farali bana, "Amma wasu gurɓatattun jagorori suka hana mafarkinsa cika," duk da ya rungumi ƙaddara ya san haka Allah ya tsara.