Abinda Ya Jawo Za'a Hana Yin Amfani Da Manhajar Ticktok A Faɗin DuniyaCikin Wata sanarwa dake yawo a kafafen watsa labarai na zamani na nuna cewa gwamnatin Amurka ta umarci kamfanin Goggle da su cire manhajar nan ta Tiktok daga cikin kundin su. 


Kamar yadda kowa ya sani shi kamfanin Tiktok na kasar China ne, wanda kowa yasan yadda Tiktok yayi barazanar kashe kasuwar manhajar Instagram da Facebook da suka kasance mallakin shahararren matashin me kudinnan dan kasar Amurka wato Mark Zuckerberg.


kowa dai yasan yadda alakar kasar China da Amurka yake na rashin jituwa da juna. Umurnin dai ya biyo bayan zarge-zargen da kamfanin na Instagram ya shigar cewa Tiktok ya masa satar fasaha, zargin da kamfanin na Tiktok yace karyace kawai tsagoranta da hassada irin ta Instagram.


Amma su basu musu satar fasahaba, su Instagram dinne ma suka sace musu sabbin fasaharsu da su kadai suka zo da wannan fasaha, a yanzu haka dai ana dambaruwa, kwanaki hudu kacal suka ragewa Tiktok a manhajar Play store ko zasu sasanta ko ya zata kaya?


Idan har Play Store suka cire Tiktok, to Tiktok na kowa zaiyi Expire hakan zai hana kowa yin amfani da shi har sai kamfanin ya canza manhaja, Google Play Store ma dai mallakin Kasar Amurka ne.”


Tun bayan fitar wannan sanarwa ne dai masu yin amfani da wannan manhajar ta Ticktok suke bayyana rashin jin dadin su. Anga tsokacin wasu daga cikin ƴan Najeriya masu yin amfani da wannan manhaja suna kokawa akan barazanar da ake yi na kokarin dakatar dashi.


Daga: Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post