Sojojin Najeriya Da Dama Ake Fargabar Sun Mutu A Wani Sabon Harin Kwantan Bauna Da Yan Boko Haram Suka Kai A Borno


Sahara Reporters sun rawaito cewa Majiyar sojoji da dama sun shaida musu  cewa an kai harin ne a karamar hukumar Gubio da ke jihar ta Borno a ranar Litinin.


An kashe wasu sojoji da ba a tantance adadinsu ba, yayin da wasu da dama suka bace bayan wani kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS, da ke yankin yammacin Afirka (ISWAP), da a da ake kira Jam’at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād a jihar Borno.


Majiyar sojoji da dama sun shaidawa jaridar Sahara Reporters cewa an kai harin ne a karamar hukumar Gubio da ke jihar a ranar Litinin.


Majiyar ta kara da cewa akalla motar soji, makamai da alburusai da dama ne ‘yan ta’addan suka sace tare da kona su a yayin harin.


Jaridar Sahara Reporters ta tattaro cewa sojojin na yin sintiri ne domin fatattakar wasu daga cikin ‘yan ta’addan na Boko Haram a yankin bayan sahihan bayan samun rahotanni na sirri wanda kuma a lokacin ne ‘yan kungiyar suka yi musu kwanton bauna.


Kungiyar ta Boko Haram a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta tabbatar da cewa sune suka kai harin kwanton bauna.


Kungiyar Boko Haram da ISWAP, da ke yankin yammacin Afirka, sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.


Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa an yi galaba a kan ‘yan ta’addan, sai dai kuma a lokuta da dama 'yan ta'addan suna fitowa suna yin watsi da duk abubuwan da sojin ke fada.


A cikin watannin da suka gabata mahara sun sha kai wa sojoji hari wanda hakan ke jawo mutuwar su da dama. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post