An Tsinci Gawar Faston Cocin Katolika Kwanaki 4 Da Yin Garkuwa Da Shi A Kaduna


'Yan bindiga sun kashe daya daga cikin faston cocin katolika a Kaduna da aka sace bayan sun karbi kudin fansar sa.


A wata sanarwa da cocin katolikan ta fitar, ta ce an gano gawar Rabaran John Mark Cheitnum a jiya Talata.


Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Kaduna ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da mutanen sun karbi kudin fansa.


Ya ce bayan da suka karbi kudin fansar sai suka yi musu kwatancen wurin da gawar faston take.


Sai dai 'yan bindigar sun saki dayan faston da suka yi garkuwa da shi wato Rabaran Donatus Cleopas.


Babu tabbaci kan dalilin da ya sa aka harbe dayan faston. An yi garkuwa da fastocin biyu ne a kauyen Yadin Garu a ranar Juma'ar da ta gabata.


Tun daga watan Mayun bana, an yi garkuwa da gwamman malaman Addinin Kirista wadanda akasarinsu mabiya dariƙar katolika ne.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post