DA DUMI-DUMI: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'an 'yan sanda 10 a jihar Nasarawa a kan hanyarsu ta dawowa daga zaben Osun


Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da jami’an ‘yan sandan jihar Nasarawa guda goma a jihar Kogi, yayin da suke dawowa daga jihar Osun.


Majiyar ‘yan sanda ta ce, “an yi garkuwa da jami’an ne a Obajana, jihar Kogi a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, a lokacin da suke dawowa daga aikin zabe.


“A ranar 17 ga Yuli, da misalin karfe 11:05 na safe, bayanai da aka samu daga jami’in ‘yan sanda na Dibisional (DPO) Obajana, sun nuna cewa an ji karar harbe-harbe a kan sabon titin  Bye pass, kusa da Trailer Park-PTI Obajana.


“Nan take DPO din ya hada tawagar ‘yan sintiri zuwa wurin, inda suka hadu da wata farar motar fasinja Baw 18 Seater Bus mai lamba GWA 295 YR, wani mai suna Usman Abdullahi, ‘m’, tare da mutane shida.


“Mutane bakwai da suka bari sun bayyana kansu a matsayin jami’an ‘yan sanda daga rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa da suka dawo daga kammala zaben gwamnan Osun.


“Jami’an sun bayyana cewa motar tasu ta samu matsala ne, wanda hakan ya sa suka fice daga cikin ayarin nasu, yayin da suke kokarin gyara motar, kwatsam wasu dauke da makamai suka fito daga cikin daji suka yi awon gaba da jami’ai goma da karfi.


“An baza jami’an da ke yaki da garkuwa da mutane yankin, inda a halin yanzu suke bin diddigin ‘yan bindigar domin ceto jami’an.


Majiyar ta kara da cewa, "A halin da ake ciki, sauran rundunonin an kwantar da su a hedikwatar rundunar."


A halin da ake ciki, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa, DSP, Rainham Nansel, har yanzu bai amsa sakonnin tes da kiran waya da aka aike ta lambar wayarsa ba a lokacin da aka fitar da labarin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post