Da Mu Da Jami'an Tsaro Mun Gaza Samar Da Tsaro A Katsina, cewar Gwamna Masari


Gwamnan jihar Katsina Rt. Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa Tabbas gwamnatinsa da jami'an tsaro sun gaza bawa talakawa tsaro a fadin jihar da ma Najeriya baki daya.


A cikin firar da aka zanta da Gwamna Masari, jaridar Katsina Post ta samu labarin yadda ya bayyana cewa;


“ko shakka babu tabbas hankalin jama'a na tashi, tinda jami'an tsaro da mu , duk talakawa da mu suka dogara domin mu kare dukiyarsu da rayukansu, tabbas an samu rauni an samu gazawa daga garemu”.


“Amma idan muka kalli meye ya kawo gazawar da kuma raunin, tinda jami'an tsaron nan da yawa wasu an kashe su, ko sati 2 ba a yi ba asistan kwamishina na 'yan sanda, da insifekta na 'yan sanda duk sun rasa ransu, har da wasu sujoji sun rasa ransu”.


Wannan abu wani al'amari ne wanda ba Katsina kadai ya shafa ba, ya shafi duk jihohin Najeriya, da makwaftanmu Nijar, da wasu sassan yankin kasashen afrika wadanda ke like da Najeriya".


An samu sauki ba kamar  ada ba, amma bamu kai inda muke son kaiwa ba, wanda muke sa ran ba zamu barwa wata gwamnati wannan iftila'i ba har sai mun magance matsalar”.


Wajibi ne mu maido wa jihar Katsina martabarta, wanda kowa zai iya shaidarmu a bangaren ilimi a kan rawar da muka taka, da bangaren lafiya da kuma muhalli, duk da bamu samu kudi ba kamar yadda gwamnatin da ta shude ta samu kudi", inji Gwamna Masari. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post