Wani abin al'ajabi da ya jawo hankalin al'umma a fadin duniya shine yadda wata Matashiyar budurwa ta auri kanta a kasar Indiya.
Ta bayyana cewa mutane suna yi mata kallon mamaki a matsayin abinda ta aikata rashin hankali ne. A cewar matashiya Bindu mai shekaru 24 a duniya wacce ta kafa tarihin auren kanta da kanta a jihar Gujarat a yammacin Indiya.
Bindu ta ce sha'awar ta auri kanta ya fara zuwar mata ne watanni uku kacal kafin bikinta a watan Yulin 2022, bayan ta kalli wani fim a Netflix mai suna "Anne With An E" labarin wata marainiya da ta jure cin zarafi tun tana karama.
Naji dadi lokacin da na dubi kaina a madubi. Ban damu da zama kamar amaren Indiya ba. Naji Kamar na ishi kaina. Cewar amaryar kanta Bindu.
Sai dai masana na cewa yawancin masu irin wannan tunani na kaunar kansu da kansu, sun taba fuskantar matsalar soyayya ce a baya.
Ko ya kuke ganin matakin budurwar?