Dan Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Kammala Karatu Da Sakamako Mafi Daraja A Landan


A ranar 19th ga watan Yuli ne dai aka yi bikin kammala karatun Mustapha Lamido Sanusi wanda babban da ne ga tsohon Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II a birnin Landan. 


Wasu hotuna dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani an hangi maimartaba tsohon Sarkin shi da abokin sa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da sauran 'yan uwa da abokan arziki a wajen murnar kammala karatun Mustapha da aka yi a Portsmouth dake kasar Ingila. 


Rahoton ya bayyana cewa Mustapha Lamido Sanusi (Imamu) ya kammala karatun nasa ne inda ya samu matsayi mafi daraja na 1st Class na fannin Tattalin arziki (Economics).


Ko a satin da ya gabata sai dan dan wasan Najeriya Ahmad Musa ya caccaki mahukunta a Najeriya akan tura ya'yan su da suke yi kasashen waje suna karatu su kuwa ya'yan talakawa suna fama da yajin aikin ASUU. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post