Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bawa Ministan ilimi Adamu Adamu tsawon makonni 2 domin kawo karshen yajin aikin ASUU da aka shafe kusan watanni 7 ana yi.
Sanarwar ta shugaban kasa ta fito ne tun ranar Talata inda ya bayar da umarni ga Ministan ilimi cewa a zauna da malaman Jami'a a sasanta da su akan abubuwan da ake takaddama dasu.
A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya samu ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi na kasar wanda ake tunanin zasu iya kawo karshen matsalar.
Rahoton ya bayyana cewa Shugaban kasar ya kira su ne domin ya samu karin bayani a kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin yaki ci yaki cinyewa.
Yanzu abin jira a gani shine Ko nan da sati 2 za'a samu kawo karshen wannan yajin aikin da aka dade ana yi? Lokaci ne dai zai tabbatar mana da hakan.