Duk Mace Tanada Bukatar Sanin Waɗannan Abubuwan Guda 6 Kafin Tayi Aure


A yau a cikin wannan rubutun za kuji wasu muhimman abubuwa 6 da ake so duk wata mace tasan su kafin tayi aure. Domin sau dayawa wasu matan suna tunanin irin yadda ake rayuwa kafin aure to irin ta ce za suyi bayan aure.


Shi aure wata rayuwa ce da ake yin ta dake dauke da wasu kalubale wanda kuma sai ma'aurata sun karance su tun kafin suyi auren domin sanin yadda za su gudanar da rayuwar auren cikin zaman lafiya da annashuwa.


Shiyasa a wannan rubutun muka kawo muku wasu muhimman abubuwa 6 da ya kamata duk mace tasani kuma tasan yadda zata gudanar dasu tun kafin tayi aure. Ga dai abubuwan kamar haka;


(1) Jin Dadi Ba Zai Tabbata Ba A Kullum;

Rayuwar aure rayuwa ce da ta kunshi jin dadi da akasin haka. Matukar mace ta sa ma ranta cewa jin dadi da rashin sa duk za ta yi karo da su a cikin auren ta, hakan zai sa ta sama ranta salama, sannan ta zauna lafiya da mijinta saboda ta san ba kullum ne zasu kasance cikin jin dadi ba.


 A ranakun da aka samu rashin jin dadi hakan zai bata kwarin gwuiwa na tsayawa mijinta ba tare da ta tuhume shi ba. Saboda bata da wannan dogon burin a rayuwar aurenta, duk yanda yazo matukar ba a shiga hakkinta ba ta kan jure tare da kauda kai.


Sannan ba za ta yi tunanin kullum sai mijinta ya faranta ma ta ba, ko kuma ya biya ma ta dukkan bukatunta. Sannan ta san cewa ba zai taba iya kyautata ma ta ba dari bisa dari ba.


(2) Ba Kullum Ne Zakiji Yanayin Soyayya Ba;

Duk irin son da kike yiwa saurayinki, daga zarar kun yi aure akwai lokuttan da za su zo ki ji cewa ba ki jin wannan soyayyar, ba kuma wai dan kin daina sonsa ba. Ko da kuwa a ce duk duniya babu wanda ya kai mjinki wajen sauke duk wani hakkin da ya rataya a wuyansa sai kin ji wata rana kin wayi gari kina cikin wani yanayi sannan ba ki jin wannan soyayyar.


A’a yanayin kasancewarku a karkashin inuwa daya ne, kullum kuna ganin juna.


Za ku kwana ku tashi tare, wasu ma’auranta ma da wuya su yi kwanaki biyar basu ga juna ba. 


Jaridar “Times of India” ta taba wallafa labarin wasu ma’aurata da kan tafi aiki na wasu kwanaki basu tare, sun bayyana cewa a duk lokacin da su ka dawo su kan ji su kamar sabbin ma’aurata hakan na sa soyayyar su kara karfi.


(3) Dangin Mijiniki  Suna Da Matukar Muhimmanci;

Iyayen miji da yan uwansa na da muhimmanci a rayuwar aurenki. Ki tafi da kyakkyawar zuciya a kansu, ki watsar da duk wani abu da mutane za su ce miki game da su. Ki bari har sai wani abu ya hada ku ta nan za ki san yanda za ki tafiyar da su cikin kwanciyar hankali. Musamman iyayen miji da suka yi sanadin kawo abun kaunarki a duniya, ba ki da kamar su. 


Duk yanda ku ka kai samun kwanciyar hankali da mijinki matukar kuna samun matsala da dangin mijinki, auren nan ya dinga tangadi kenan, ke kanki ba za ki samu kwanciyar hankali ba. Tun mijin na goyon bayanki za a zo lokacin da zai fara dora laifin a kanki.


(4) Samun Sabani Abune Dake Faruwa, Kuma Ba Za'a Iya Guje Masaba;

Mace ta sa ma ranta cewa dole a rayuwar aure a rika samun sabani, amma mi? Ki san matakan da za ki bi wajen magance wannan sabanin. A duk lokacin da a ka samu sabani, ke a matsayin ki ta mace ki saukar da kai, sannan ki samu lokaci na musamman wajen tattauna matsalolinku. Kowane aure da irin matsalolin da yake fuskanta da kuma yanayin yanda ake warware shi.


Ko da kuna da matsala iri daya da wata, yanda za ta warware tata matsalar ya sha bambam da yanda za ki warware ta ki, saboda kowane mutum da irin dabi’arsa.


(5) A Lokacin Da Tafiya Take Yin Tsawo A Lokacin Ne Kuma Komai Ke Daukar Zafi;

A irin wannan yanayin wasu matan aurensu ke mutuwa, musamman tsakanin shekara daya zuwa biyar. 


Akwai wata dabi’a ta mata a wannan zamanin ta rashin juriya, da kuma duk matsalar da ta tunkaro aure maimakon a magance ta sai kawai a nemo hanyar raba auren. Kalubale da matsaloli suna daga cikin ababen da ke kara ma aure karko, saboda a lokacin da suke faruwa a lokacin ake nemo hanyoyin  warware su ake kara sanin juna.


(6) Zaman Aure Hakuri Da Juriya Shine Ke Tafiyar Dashi;


Mafi yawan lokuta akan jaddada ma mace cewa aure ibada ce ta hakuri. Duk inda za ka zauna, zaman kuma ya wuce na mutum daya ya zama wajibi kayi hakuri, bare kuma rayuwa ta aure da kaso mafi yawa a ciki hakuri da juriya ne.


Duk yanda aka kai ga kwatantawa mace yanda hakuri yake a gidan aure ba za ta fahimci me ake nufi ba sai ta shiga daga ciki.


Duk yanda ku ka kai ga son junanku dole ku samu sabani a tsakanin wanda hakurin zai tafiyar da komi.


Babban dalilin da yasa aure a zamanin baya yafi karko da aminci kenan saboda hakurinsu, wanda yayi karanci a wannan zamanin, babban dalilin da ke kawo mutuwar aure.


Wannan sune wasu daga cikin abubuwan da ya kamata duk mace tasani kafin tayi aure domin sanin yadda zata iya zaman aure cikin hakuri da jindadi ba tare da samun matsala ba. Da fatan ma'aurata za'a ringa yin hakuri da junansu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post