Ba Zaiyu A Sake Zabar Musulmai 2 A Jihar Kaduna Ba


Kungiyar Kabilun Kudancin Jihar Kaduna (SOKAPU), ta ce a zaben 2023 sam ba za ta taba sabuwa a sake yin tsarin zabar musulmai biyu a matsayin gwamna da mataimaki ba. 


A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Luka Binnyiyat, ta fitar a jihar ta ce ba zasu sake marawa ‘yan addini daya baya ba.


Sanata Uba Sani, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na facebook a ranar Litinin, na tabbatar da daukar Mataimakiyar Gwamna jihar mai ci a yanzu, Dakta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa.


Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yi ammana da cewa, a bangarorin biyu na jihar akwai Kiristoci da Musulmai da suka cancanta wanda kuma suka fi dace wa a dauka a matsayin mataimaka a kowace jam’iyyar siyasa.


A cewar sanarwar gwamna El-rufai na sane da cewa yawan al’ummar da ke a kudancin kaduna ba su kai yawan adadin Kiristocin da ke a yankin ba.


Sanarwar ta kara da cewa, “Ba wai muna kin jinin Dakta Hadiza bane, amma ya kamata a yi adalci kuma sake daukarta a matsayin mataimakiya kamar cin fuska ne a gare mu.”


Rahoto Daga Daily Trust Hausa

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post