Yanzu-Yanzu: Abba Kyari, Dariye, Nyame sun tsere daga magarkamar gidan yarin Kuje


Ana tunanin wasu manyan fitattun fursunoni a gidan yari na Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata.


Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkamar, a harin da ya dauki tsawon sa’o’i, an ce jami’an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.


Legit.ng ta rawaito cewa, haka ma tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na Taraba Jolly Nyame da majalisar kasa ta yi wa afuwa a baya-bayan nan.


Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da sakin su Dariye ba har aka samu akasi aka kai hari magarkamar.


Majiyoyi a cikin magarkamar sun shaidawa jaridar The Nation cewa baya ga manyan fursunonin, wasu ‘yan ta’adda da sauran masu laifi sun tsere yayin da maharan ke luguden wuta.


Sai dai har zuwa lokacin da hada wannan rahoto, babu wani tabbaci a hukumance kan adadin wadanda suka tsere da bayanansu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post