An kashe wata matashiya a cikin hotel aka caka mata wuka akan ₦1000 a Sokoto


An cafke wani mutum da ake zargin sa da kashe wata mata mai zaman kanta a unguwar Kwanawa ta karamar hukuma Dange/Shuni a Jihar Sokoto.


Isyaku.com ya rawaito cewa wanda ake zargin ya cakawa matar wuka ne a sakamakon takardama da ta kaure a tsakanin su bayan ya bata dubu 1000 ladan lalatar da suka yi inda taki amincewa da hakan hakan yasa ya caka mata wuka.


Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar Punch  cewa, wacce aka kashen tana zaune ne a daya daga cikin gidajen karuwai da ke yankin da aka sansu da duk wani nau’in haramun. 


Wata majiya ta ce karar da makwabtan da ke kusa da otal din da masu wucewa suka ji ne ya ja hankalin mutanen da suka kama wanda ake zargin a lokacin da ya yi yunkurin guduwa bayan ya gano cewa wanda ya caka wa wuka ta mutu.


Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Sanusi Abubakar, wanda ya tabbatar wa jaridar Punch faruwar lamarin, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi mai bincike ne da ya ziyarci Jihar Sakkwato domin gudanar da bincike.


Abubakar ya ce wanda ake zargin ya yanke shawarar kwana tare da karuwar amma ya ce matsalar ta fara ne lokacin da wanda ake zargin ya biya wacce aka kashe Naira 1,000.


Jami’in PPRO ya ce wanda abin ya shafa ta ki amincewa da kudin, wanda hakan ya haifar da fada a tsakaninsu.


A cewar kakakin, wanda ake zargin ya fito da wata wuka ya yi amfani da shi wajen daba mata bayan ya rinjaye ta.


Abubakar ya kara da cewa an mayar da shari’ar zuwa sashin kisan kai na rundunar domin gudanar da bincike mai kyau. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post