Mu Dauwarawa Muna Alfahri Da Buhari Saboda Ya Kawo Ci Gaba A Nijeriya - Sarkin Daura


Sarkin Daura ya bayyana shugaban ƙasa general Muhammad Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba abin alfahari wanda baza'a manta dashi ba.


Sarkin yace su mutanen Daura suna alfahari da Buhari duba da irin cigaban da ya kawo a kasa Najeriya. Inda yace duk ɗan Daura yana alfahari da irin cigaban da shugaban ya kawowa kasa Najeriya.


Sarkin ya bayyana hakan ne a jawabin sa na shagulgulan Sallah da ake gabatarwa wanda shima shugaban ƙasa Buhari yaje Daura domin yin bikin Sallah.


Ko a ranar Idi ma an hangi dubban jama'a bayan sallar Idi suna ta yiwa shugaban fatan alheri inda suke ta daga masa hannu tare da yi masa addu'a da fatan Alheri. 


Hakan ya nuna al'ummar garin Daura har gobe suna tare da shugaban ƙasa Muhammad Buhari duk kuwa da yanayin da ake ciki na halin Ƙuncin rayuwa wanda ake zargin cewa tsarin tafiyar da mulkin sa shine ya haddasa hakan.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post