Ƴan Boko Haram Sun Kai Wani Mummunan Hari A Wani Asibiti Inda Suka Kone Shi Suka Sace Kayan Amfani


Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a asibitin Mada da ke yankin Arewa mai Nisa a kasar Kamaru cikin daren Juma’a zuwa Asabar.


Jaridar VOA ta rawaito cewa, an kashe wani mai gadi a wannan asibitin tare da jikkata wasu ma’aitakata da kuma marasa lafiya da dama masu jinya a wannan asibiti.


Boubakari Ahmadou daya daga cikin wadannan suka tsira daga wannan aika-aika ya shaidawa muryar Amurka cewa “Mayakan Boko haram sun iso cikin dare tun daga kofa suka soma harba bindiga. Muna daga ciki mu ka hango yadda suke zuba man fetur a jikin gini, da mai gadi ya nemi ya tsare su sai suka kashe shi.


Bayan haka suka kona asibiti. Suka kuma dauke kayan abinci da aka tara a asibiti saboda marasa lafiya. Zuwan sojojin Kamaru ne ya sa suka zabura, suka tsere daga wajen”.


Maharan sun kuma kona asibitin Mada kurmus. Haka zalika suka kona motocin daukan marasa lafiya da babura.


Wata kungiya mai zaman kanta Humanity Purpose ta ce, an yi garkuwa da wasu sojojin Kamaru a yayin harin, amma babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da wannan garkuwar.


Boubakari ya kara da cewa “A wannan yankin Mada, tun da matsalar Boko Haram ta bayyana, muna fiskantar hare-hare a kowace damuna. Saboda yanayi na sanya jami’an tsaro su koma daga cikin manyan kauyuka saboda hanyar zuwa Mada bata da kyau.


Da duk kokarin da hukumomin mu suke yi, dole ne jami’an tsaro su koma da baya. Muna fatar gwamnati za ta mai da hankali kan wannan yakin bayan wanan hari da Boko haram suka kai”


A 'yan watannin da suka gabata kungiyar Boko Haram ta kara kai hare-hare a yankin Arewa mai nisa inda yanayin tsaro ya yi karanci 'yan kwanakin nan.


Shugaban kasa Paul Biya ya aika da ministar da ke kula da harkokin tsaro, Joseph Beti Assomo zuwa yankin arewa mai nisa, domin farfado da sojojin, da kuma kara musu kwarin gwiwa da nufin shawo kan wannan matasala.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post