Al'ajabi: Kare ya ɗauki rainon marayun ƴaƴan agwagwa 15 bayan mahaifiyarsu tayi ɓatan dabo


A wani yanayi na jin tausayi da jin-ƙai, wani kare mai ban sha'awa, mai suna Fred, ya ɗauki rainon wasu marayun ƴaƴan agwagwa su 15, bayan mahaifiyarsu ta ɓace ba zato ba tsammani.


Wani rahoto da jaridar Daily Nigerian ta fitar ya bayyana cewa Fred, mai shekaru 15, ya yi suna wajen rainon dabbobi ƴan'uwansa. A shekarar 2018, Fred ya game kafafen yaɗa labarai bayan da ya raini wasu marayun ƴaƴan agwagi guda tara da aka watsar a cikin irin wannan yanayi.


Shekaru bayan nan, tsohon karen ya kasance baya-goya-marayu ga ƴan'uwansa karnuka. Wasu hotuna da su ka kewaye kafafen sadarwa sun nuna ƙananan ƴaƴan agwagin a durƙushe a tsakanin kafafun Fred, inda wasu kuma su ka ɗare bayansa cikin wani yanayi na shaƙatawa, yayin da suke kwance tare a rana.


Ƴaƴan agwagin, masu launin ɗorawa, hotonsu ya bayyana inda su ke kwance a bayan Fred wanda shi ne sabon uba a gare su. Fred mazaunin Mountfitchet Castle ne kusa da Stansted, Essex, inda mahaifiyar ƴaƴan agwagin ta ɓace cikin dare.


Tun daga wannan lokacin, Fred ya ɗauki gaɓaren kula da su inda ya goya su a bayansa yana ɗauke da su yana nuna su ga ma'aikata da baƙi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post