Da Dumi-Dumi Ƴan bindiga sun kashe “Area Commander“ na 'yan sanda a Katsina


Mahara sun kashe babban kwamandan ‘yan sanda a yankin Dutsinma da ke Katsina, ACP Aminu UMar. Sanarwar da rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta fitar ta ce ACP Aminu ya rasa ransa tare da wani dan sanda guda daya bayan wata arangama da suka yi da barayi a dajin Zakkah da ke cikin karamar hukumar Safana. 


Jaridar DW Hausa ce ta wallafa labarin rasuwar jami'in ɗan sandan a shafin ta na facebook. Sai dai basu bayyana dalilin rasuwar tasa ba. Sai dai sunce suna gudanar da bincike domin gano musabbabin yadda ƴan bindigar suka kashe shi.


Kafin sadaukarwar da ACP Aminu ya yi a ranar Litinin da daddare ya kasance jajirtaccen dan sanda; mara tsoro, a cewar abokan aikinsa.


Hare-haren ƴan bindiga dai tare da kashe jami'an tsaro a jihar Katsina ba sabon abu bane. Ko a farkon shekarar 2022 sai da wasu mahara suka kashe wani baturen dan sanda a ƙaramar hukumar jibia.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post