Makomar Shirin IZZAR SO Bayan Rasuwar Daraktan Shirin Nura Mustapha


Lawal Ahmad (Umar Hashim) Ya Bayyana Makomar Shirin IZZAR SO Bayan Rasuwar Daraktan Shirin Nura Mustapha Waye Wanda Ya Rasu Ranar Asabar.


A wata hira da aka yi da Lawal Ahmad, an tambaye shi Kan cewa shirin na IZZAR SO ya tsaya kenan ko kuma za'a ci gaba da yin sa?


Lawal Ahmad ya bada amsar cewa. Yanzu suna cikin jimamin rasuwar Nura don haka babu wata amsa da zan iya baka daga wannan tambayar da kaimin.


Anaci gaba da ta’aziyya tare da jimamin rashin babban darakta na KannyWood da Kuma shirin nan mai farin jini na dogon zango IZZAR SO. 


Nura Mustapha Waye, wanda Allah ya karbi kwanansa ranar Asabar 2/7/2022, wanda aka rawaito cewa babu wata cuta dake damunsa asali ma lafiya lau ya kwanta amma kuma aka wayi gari babu shi.


Jarumai da waɗanda ba jarumai ba sun ci gaba da miƙa ta’aziyyar su  ga iyalai da kuma abokanan aikin mamacin. 


Bayan rasuwar ne Kuma mutane da dama suke tunanin yaya makomar shirin na IZZAR SO zai kasance, duba da yadda ake ganin labarin film ɗin shine yake bada umarnin sa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post