Wasu hotuna da Jarumar Ƙannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta fitar sun ɗauki hankalin al'umma a kafafen sadarwa na zamani.
Domin ba'a saba ganin ta tana irin wannan hotunan ba. Amma hakan baya rasa nasaba da bikin zagayowar ranar haihuwar ta wanda tayi hotunan domin nuna murna da farin ciki.
Jama'a dai na ta yima ta fatan alheri tare da taya ta murnar bikin zagayowar ranar haihuwar ta. Cikin masu taya ta murnar kuwa har da abokanan sana'ar ta na Kannywood inda suke wallafa hotunan ta domin taya ta murna.