An Saka Ranar Auren Mawƙi Lilin Baba Da Jaruma Ummi Rahab


Fitaccen Mawaƙi, Shu’aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya biya kuɗin auren jarumar Fina-finan Kannywood Ummi Rahab har an sa ranar da za'a ɗaura auren nasu.


Abokin Mawaƙi, Suleiman Sa Zizou ne ya sanar da haka a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta cewa, “Mun biya sadaki kuma an saka rana Alhamdulilahi ya Allah! An gama magana. Ina taya ku murna.”


Sai dai har kawo zuwa wannan lokacin ba'a faɗi ranar da aka sa za a ɗaura auren ba, kamar yadda Zizou ya wallafa a shafin nasa. Amma daga baya anga wani katin gayyata yana ta yawo akafafen sadarwa na zamani, wanda yake nuna ranar da za'a yi ɗaurin auren masoyan.


Sanarwar ta bayyana cewa za'a yi ɗaurin auren ne ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 2022 a tudun Murtala dake ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post