Idan Kika Samu Namiji Mai Irin Wannan Halayen Ki Riƙeshi Karkiyi Wasa DashiKaman yadda muka kawo wasu alamu na dacen mijin aure kamin mace ta amince da mai sonta da aure, ga Karin wasu alamomin da suke tabbatar miki da kinyi dacen mijin aure:


Sai dai ba duka ne ƴan mata suke ɗaukar masu irin wannan halayen da muhimmanci ba sai bayan sun rabu daga baya ta yi nadama. Shiyasa muka yi muku wannan rubutun na musamman domin kusan darajar maza masu yi muku waɗannan abubuwan.


(1) Namijin da ya damu da damuwarki.

(2) Namijin da kullum sai ya kiraki ya tambayeki yadda kika kwana, kika wuni da kuma yi miki fatan tashi lafiya.

(3) Namijin Da Yake Baki Lokaci Baya fakewa da aiki yayi masa yawa.

(4) Namijin da yake sauraronki yake baki hankalinsa a duk lokacin da kike son zantawa dashi na muhimmi.

(5) Namijin da baya jira har sai kin tambayeshi.

(6) Namiji mai cika alkawari. Duk alkawarin da ya miki yana kokarin ya cika. Bana naki kadai ba har na wasu daban. Wannan ba mijin yadawa bane, rike shi gam.

(7) Namiji mai furta miki kalaman so a fili, a baka da kuma kuna ku biyu.

(8) Namiji mai kalamai masu kyau a lokacin farin ciki da kuma bacin ransa.

(9) Namijin da yake da zumudin bashi dama yaga iyayenki ko magabatanki.

(10) Namiji mai nuna miki farin cikinsa da kuma yi miki godiya a duk lokacinda kika yi abun ayaba miki. Da kallon kwalliyarki ya yaba. Idan kin kawo masa ruwa ko abinci ya jisu daban da wadanda ya saba.

(11) Namiji mai amafni da wadannan kalmomin guda biyu, magiya idan zai saki masa wani abun. Ya kuma ce ya gode idan kika masa, (please and thank you).

(12) Namijin da baya kunyar a ganki da shi.


Da fatan mata zasu kula da irin waɗannan mazajen, domin sune abin nema. Kuma koda kin aure shi haka zai ringa yi miki ko kuma ya ƙara. Muna addu'ar Allah ya bawa mata mazaje nagari masu kulawa da su da saka su farin ciki. Suma mazan Allah ya basu mata nagari.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post