Za'a Samu Ƙarin Kuɗin Biredi A Najeriya Sakamakon Tsadar Man Fetur Da Fulawa


Masu masana'antu a Najeriya suna cigaba da kokawa akan hauhawar kayan sarrafawa a sakamakon cigaba da tsadar man fetur da man dizal. Ƙungiyar dillalan man dizal a ƙasar ta yi gargadin cewa matuƙar hukumomi ba su ɗauki matakin da ya dace ba, to farashin makamashin zai kai wani matsayi da ba a taɓa gani ba a Najeriya.


Ƙungiyar masu gidajen burodi a Abuja ta ce akwai yiwuwar farashin burodin zai ninka kuɗinsa nan gaba kaɗan, bayan sun sayi litar dizal a kan naira 1,500 a ranar Laraba.


Mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeriya Alhaji Ali Safiyanu Madugu ya ce ya kamata gwamnati ta shiga lamarin tun kafin abin ya kazance.


Shi kuwa Alhaji Ishaq Abdulraheem shugaban masu gidajen biredi na birnin Abuja cewa yake sun shiga halin ni ‘ya su, saboda, baya ga tsadar man dizal din akwai kuma tsadar kayan sarrafa burodin.


Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN dai, tace wannan matsalar tana da nasaba da abubuwa da dama ciki har da tsadar dala da yakin Ukraine da Rasha sai kuma zargin da suke yi cewa hukumar kula da sufurin man fetur ta Najeriya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post