Ƴan Fashin Daji Sun Nemi A Basu Kuɗaɗe Miliyan 145, Kafin Su Saki Mutanen Da Suka Yi Garkuwa Dasu A Zamfara


Rahotanni daga yankin arewa maso yammacin Najeriya na bayyana cewae, ƴan ta’adda ko kuma sun nemi a biyasu maƙudan kuɗaɗe da yawansu ya kai akalla naira miliyan 145, kafin su saki mutane kusan 30 da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.


Kafar talabijin na Channels dake Najeriya ya ruwaito cewa sakataren ƙungiyar wadanda abin ya shafa na jihar Zamfara Ashiru Zurmi, na cewa ƴan bindigar na tuntubar kungiyar tasu, ta hanyar amfani da daya daga cikin wayoyin wadanda suka yi garkuwa da su, inda suka bukaci da a biyasu makudan kudaden da suka nema a matsayin kudin fansa.


Tun a ranar Asabar da ta gabata ne dai, ƴan bindiga suka sace mutane fiye da 50 a yankin Dogon Awo dake tsakanin Bakura da Tureta a kusa da iyakar Sokoto. Bayanai sun ce yawan mutanen da ƴan ta’addan suka sace na kan hanyar su ta komawa gidajensu dake Zamfara ne daga wani bikin aure da suka halarta a jihar Sokoto.


Sai dai jim kaɗan bayan fadawa hannun maharan wasu daga cikin matafiyan da adadinsu ya zarce 20 suka samu nasarar tserewa, inda bayanai suka ce jami’an tsaro ne da kuma ƴan Bijilan suka ceto wasunsu.


Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar tsaron ta’addancin ƴan bindiga masu kisa, garkuwa da mutane da kuma sace dimbin dukiyar jama’a, matsalar da ta tilastawa dubban mutane yin gudun hijira daga kauyukansu zuwa cikin birane, yayin da wasu ma ke tsallakawa cikin Jamhuriyar Nijar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post