Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Bayyana Cigaban Da Zai Kawo A Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa


Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Bayyana Cigaban Da Zai Kawo Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa a Najeriya.


Dr Rabiu Kwankwaso wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma tsoho ministan tsaro ne ya kuma ce zai ɓullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da ƙasar gaba.


Sannan a ɓangaren Ilimi yaci alwashin cewa kamar yadda ya ɗauki nauyin kai matasa karatu zuwa ƙasashen waje, da zarar ya zamo shugaban kasa zai ɗora daga inda ya tsaya tare da mayar da ilimin cikin gida daga Firamare har zuwa Jami'ah kyauta.


Haka kuma Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka abisa yadda har yanzu ɗaliban ƙasar nan suke zaman gida sama da wata biyar saboda yajin aikin malaman Jami'oin ASUU wanda yaƙi ci yaƙi cinyewa.


Sanata Kwankwaso yana ɗaukar waɗannan alkawura ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP mai kayan marmari a babbar birnin Calabar a jihar Cross River.


Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na siya, suna bayyana ɗan takarar a matsayin wanda ba lallai ne yai nasara a zaɓe mai zuwa ba, duba da irin jam'iyar da yake yin takarar a cikin ta sabuwa ce.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post