Ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok ta sheƙi iskar yanci bayan shafe Shekaru 8 a hannun ƴan ta'ada


Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta ceto wata yarinya Mary Ngoshe, wadda ake kyautata zaton tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace daga makarantar Sakandaren ƴan mata ta gwamnati ta Chibok, a jihar Borno.


Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba ta sahihin shafin ta na Twitter na rundunar sojojin Najeriya, ‘@HQNigerianArmy,’. Rundunar ta ce dakarun rundunar sojoji ta bataliya ta 26 da ke sintiri a kewayen Ngoshe, a Borno sun kama wata mai suna Ngoshe da ɗanta.


Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa ana kyautata zaton matar tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace daga GGSS Chibok, a cikin 2014. Ana ci gaba da bincike a kan lamarin," in ji bayanin.


Rundunar ta kara da cewa: “A ci gaba da farmakin da dakarun Operation Desert Sanity, tare da hadin gwiwar CJTF suka yi, sun sake yin wata gagarumar nasara a ranar Talata. "Wannan ya kasance yayin da aka kashe 'yan ta'addar ISWAP a kusa da Gurzum, a Borno.

 

“An lalata kasuwar ‘yan ta’adda da sansanoni. An kwato makamai, da sauransu,” a cewar bayanin. Sai dai har kawo zuwa haɗa wannan rahoton babu adadin da rundunar soji ta bayar na waɗanda suka rasa rayukansu.


Jihar Borno dai ta jima tana fama da hare-haren ƴan bindiga na Boko Haram da ISWAP wanda ya haddasa mutuwar dubban mutane tare da dukiyoyi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post