Yadda tarin jama'a ke guduwa daga Ƙauyen Mada na Jihar Zamfara bayan harin ƴan bindiga


Bayanai daga garin Mada na Jihar Zamfara na cewa mutane na tserewa daga garin bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a ranar juma'a.


Jaridar BBC Hausa ta rawaito cewa ƴan bindigan sun harbi mutum ɗaya sannan suka tafi da wasu mutum huɗu baya ga ɗumbin dabbobi da suka kora suka tafi dasu.


Sai dai shaidun sun ce sojoji na dakatar da mutane da ke tserewa domin barin garin, inda suke hana su ficewa, lamarin da ya jawo mazauna Mada ke zanga-zanga domin a kuɓutar da garin daga hannun ƴan bindiga.


Jaridar ta BBC ta ce ta tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara domin ji daga gare shi, amma har zuwa wannan lokacin bai amsa kiran wayar ba.


Wannan hari dai, shi ne irinsa na uku a cikin kwana uku a jere da ƴan bindiga ke kaiwa garin na Mada da wasu garuruwan dake makwabta da su.


Hare-haren ƴan bindiga dai a jihar Zamfara sai ƙara ƙamari yake yi inda kusan kullum sai kaji labarin kai hari a wasu ƙauyukan jihar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post