Gwamnatin jihar Zamfara ta bada umarnin Mallakar bindiga ga ƴan Jihar domin kare kansu daga ƴan bindiga


Sakamakon fama da hare-haren ƴan bindiga da ya addabi al'ummar Jihar hakan yasa gwamnatin za ta bayar da izinin mallakar bindiga domin mutane su kare kansu daga ƴan bindigar.


Cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara, gwamnatin Zamfara ta ce ofishin kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ne zai tantance mutanen da suka cancanci mallakar bindigogin don kare kansu, musamman manoma dake a yakunan karkara.


Haka kuma sanarwar ta kara da cewa za'a kafa cibiyar tattara bayanan sirri kan ayyukan masu taimakawa ‘yan bindiga da bayanai.


Sannan kuma gwamnatin ta umarci majalisar dokokin Jihar da ta gaggauta nazartar dokar hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama da laifin taimakawa ‘yan ta’adda da bayanai.


Daga karshe ta kuma yi gargadi mutane da su tabbatar da gaskiyar dukkanin wasu bayanai da za su gabatarwa gwamnati kan wadanda suke zargi da tatimakawa ‘yan bindiga, domin kaucewa tafka kura-kurai.


Hakazlika duk mutumin da ya ba da bayanan da ba sahihai ba kan wani, to fa za a yi masa hukunci iri daya tare da maitaimkawa ‘yan bindiga da bayanai.


Jihar Zamfara dai na fama da matsalolin tsaro wanda ya kama da hare-haren ƴan bindiga da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa. Sai dai gwamnatin jihar na ganin cewa jami'an tsaro ba za su iya kawo karshen lamarin iya su kaɗai ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post