Kamaye Yafito Yai Bayani Game Da Rashin Lafiyar Sa Da Kuɗin Da Ake Cewa Hamisu Breaker Ya Bashi


Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye, ya fito ya karyata labarin da ake yadawa na cewa bashi da lafiya kuma Hamisu Breaker da Ahmed Lawan sun bashi kyautar kudi domin yaje asibiti.


Kamaye wanda aka fi sani a cikin shirin wasan kwaikwayon nan mai dogon zango wato "Dadin Kowa", ya karyata labarin da ake yadawa na cewa yana fama da matsananciyar jinya.


Wani rahoto na cewa a sakamakon rashin lafiyar ce ta sa fitaccen mawakin nan Hamisu Breaker ya ba shi kyautar Naira Miliyan biyu. Haka shi ma Ahmed Lawan, a cewar rahoton, ya ba shi Naira dubu dari biyu don ya nemi Magani.


Bayan hirar da gidan Jaridar Aminiya suka yi dashi, Kamaye ya ce lafiyarsa kalau. A ranar Alhamis na dawo daga Jamhuriyyar Nijar cikin koshin lafiya, kwanana shida a can.”


Sannan ya kara da cewa, “Ni ban san ma an yi ba, sai bayan da wata daga Saudiyya ta turo min bidiyon da aka saka a intanet. Ni babu abin da ya same ni, kuma Breaker bai bani ko kwabo ba.”


Dan Azumi Baba ya yi Allah wadai da wannan labarin karya, ya kuma ce, ya sa a nemo mishi wanda ya kirkiri wannan karyar.


Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kirkirar mutuwa ko rashin lafiya a kakabawa jaruman finafinai wanda daga baya a gano ba haka abin ya ke ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post