Innalillahhi: Yadda Wani Manomi Ya Cire Idon Matashin Yaro Ɗan Shekara 16 A Bauchi


Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta ce an gano wani yaro ɗan shekara 16 a wani daji inda aka cire idanunsa biyu a Dutsen Jira, unguwar Yelwa a cikin birnin Bauchi.


Ahmed Wakil wanda shine Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce: “Da misalin karfe 1:00 na dare, mun samu kira daga Hakimin gundumar Birshi, Mohammed Lawal, cewa an gano wani yaro ɗan kimanin shekara 16 a cikin jini an cire idanunsa guda biyu a Dutsen Jira da ke Unguwar Yelwa a cikin birnin Bauchi.


Tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO a Yelwa ta je wurin da abun ya faru inda aka dauki yaron zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBUTH) domin yi masa magani.”


Wakil ya ce binciken farko ya nuna wanda aka cire wa idanu Uzairu Salisu mazaunin Kwanan Gulmammu Jahun Quarters ne. Wani mazunin unguwar ya shaida wa ‘yan sanda cewa wani Ibrahim da ke yankin Rafin Zurfi “wanda ya san shi ya kai shi wani daji domin ya yi aiki a gonarsa, wanda ake zargin, Ibrahim ya yi amfani da igiyar ruwa ya datse idonsa biyu. ”


‘Yan sanda sun ce yaron yana karbar magani a asibitin ATBUTH kuma sun ba da tabbacin cewa sakamakon binciken da ta gudanar za'a bayyana wa jama’a.


“Don haka kwamishinan ‘yan sanda Umar Mamman Sanda, ya jaddada bukatar iyaye da masu kula da yara da su rika sanya ido sosai a cikin unguwanninsu. 


Shugabannin al’umma, dattijai da masu mulki su kuma tabbatar da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a cikin muhallinsu tare da tabbatar da sa baki da ake bukata kafin al’amura su lalace.


“Ya kuma umurci ‘yan jihar da kada su yi kasa a gwiwa wajen hada kai da ‘yan sanda, musamman masu bayar da bayanai, da su ci gaba da taka-tsan-tsan, tare da kai rahoto ga ‘yan sanda duk wani abin tuhuma ko rashin fahimta.”

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post