Ƴan ta'adan ISWAP sun kusta kai cikin sansanin sojoji sun sace manyan makamai a Borno


Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan ISWAP ne, sun kai wa sansanin sojoji farmaki a daren Laraba a jihar Borno. Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda hatsabiban suka kai wa dakarun hari a ƙauyen Ajire cikin karamar hukumar Mafa misalin karfe 9:00 na dare, wanda hakan ya tilastawa sojojin gudu domin kare kansu daga harin ba tare da mayar musu da martani ba.


Rahoton ya bayyana cewa Kimanin soji 80 suka gudu a yayin kai harin inda suka bar tarin makamai masu tarin yawa wanda maharan suka yi awon gaba dasu. 


Rahoton ya bayyana yadda Sojojin suka kasa yin fito na fito da ƴan bindigar saboda rashin kayan harbi a hannun su. Sojojin dake da makamai a hannun su ba su da yawan da za su tinkari ƴan bindigar wanda yasa aka fatattake su


Mazauna yankin sun bayyana yadda ƴan ta'addan suka kai farmaki ƙauyen Ajire tsakanin karfe 9:00 na dare zuwa karfe 4:00 na yammacin Alhamis, sai dai basu kai hari ga mutanen yankin ba, amma an ga yadda suke tattara muhimman abubuwa a sansanin sojojin suna fita dasu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post