Burina Ya Gama Cika Tunda Nashiga Kannywood Kuma Nayi Film Da Adam A Zango


A wata hira da gidan BBC Hausa suka yi da jaruma Maryam Shuaibu Usman(Meerah) wacce ake kira da Junaidiyya a film ɗin GIDANBADAMASI ta bayyana dalilin da yasa ta shiga harkar finafinan Hausa.


Maryam dai ta bayyana cewa an haife ta ne a garin Jos kuma a can ta taso tai karatu da rayuwar ta. Kuma a can ne ta yi aure har ta haifi ɗa.


Ta bayyana cewa tun tana yarinya take da burin shiga harkar finafinan Hausa wanda kuma yanzu burin ta ya cika kamar yadda ta bayyanawa gidan BBC Hausa.


Jarumar ta fara fitowa ne a Film ɗin ta na farko da ake kira da "Ƙauran Mata" na Ahmad Shanawa wanda kuma daga bisani aka ɗauke ta a film ɗin GIDANBADAMASI da ake haskawa a tashar Arewa 24.


Koda ake tambayar ta dalilin da yasa ta kashe auranta domin ta shiga film, jarumar ta bayyana cewa ba haka bane. Tace tayi aure ne ba don ta rabu da mijinta ba. Tace haka Allah ya ƙaddara cewa zata rabu da mijinta.


Jarumar ta bayyana cewa a yanzu burin ta ya cika tunda tayi film kuma tayi da babban jarumi wanda ta daɗe tana son yin Film dashi wato jarumi Adam A Zango.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post