Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Mahaifiyar Ɗan Takarar Sanata A Jihar Jigawa


Wasu da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun sace mahaifiyar ɗan takarar sanata a jam'iyar APC mai wakiltar mazabar Jigawa ta tsakiya mai suna Tijjani Ibrahim Gaya.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, an sace Mahaifiyar sanatan ne mai suna Hajiya Jaja ƴar kimanin shekara 70 a gidanta da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar ta Jigawa.


Kakakin Rundunar ƴan Sandan Jihar, DSP Lawan Shisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata, ya ce an sace tsohuwar ce da daren ranar Litinin.


Ya ce maharan sun yinwa gidan nata ƙawanya ne sannan suka yi awon gaba da ita ta karfin tsiya. Ya ce jim kadan da samun rahoton ne Kwamishinan ƴan Sandan Jihar ya ba da umarnin baza jami’ansu don ceto ta.


Kakakin ya ce ko da yake ya zuwa yanzu ba su kai ga kama ko mutum daya daga cikin wadanda ake zargin ba, amma za su kubutar da ita, inda ya roki hadin kan jama’a wajen samar da bayanai.


Rahotanni dai sun nuna cewa maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 15 zuwa 20 sun sace ta ne bayan sun yi harbe-harben da ya tsorata mutane, sannan suka tafi da ita wajen da ba a kai ga tantancewa ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post